
An cafke wasu jami’ai da laifin safarar miyagun kwayoyi a Legas
Jaridar Tvcnews sun ruwaito Jami’ai masu kula da shige da fice na miyagun kwayoyi sun cafke wasu abokanan aikinsu dake sayarwa daiban Jami’a.
Mai sayar da kwayoyin dai wanda ke aiki da jami’an shige da fice na miyagun kwayoyi dake Legas ya shiga hannu ranar Laraban data gabata bayan yawon rangadi da jami’an suke you shaguna.
KARANTA:- Wata budurwa ta boye kanta ta bukaci 500,000 kudin fansa
Jami’an dai suna binciken shaguna lokacin da suka shiga shagon wata mata wadda ita matar jami’in sune.
Ogah Dan achaba ne daya daga cikin yaransa masu sayar masa da kwaya an bishi har inda yake inda aka kamashi da muggan kwayoyi da dama
Bayan cafke wadanda ake zargi da aika aikar Dalibai dake jami’a sun rufewa hanyar da jami’an zasu shiga.
Jagoran jami’an ya samu nasarar fidda wadan da ake zargi cikin daliban ba tare da wani hargitsi ba.
Adelodun Kamaldeen shima daya daga cikin jami’ai masu kula da shige da fice na miyagun kwayoyi dake Oyo an cafke shi ranar 13 ga watan Yuni dai dai lokacin da yake rike da wasu muggan kwayoyi.
Bayan wadannan sama jami’an suyi kokarin cafke mutane da dama tare da miyagun kwayoyi.
Shugaban rundunar yace” duk wadanda suke gani zasuyi anfani da wannan damar wajan kawo matsala a kasar Najeriya ta hanyar shige da fice na miyagun kwayoyi dasu koma su kara tunani. Domin lallai jami’an mu bazasu raga musu ba, kuma zasu kamasu zakuma su bayyana sannan zasu kwace kayan su basu hukunci daidai da aikinsu.