‘Yan bindiga sun sake yin yunkurin sace mutane a karo na biyu a rukunin gidajen ma’aikatan filin tashi da saukar jiragen sama na Kaduna a arewacin Najeriya.
Sun kutsa makarantar ne da sanyi safiyar Lahadin nan, amma kuma sojoji suka bata shirinsu na yin awon gaba da dalibanta, a cewar kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan.
Aruwan ya bada tabbacin cewa dukkannin dalibai 307 na makarantar su na nan.
Wannan lamari na zuwa ne kwanaki 2 bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan kwalejin nazarin ayyukan gandun daji da ke Afaka, karamar hukumar Igabi ta jihar Kadunar.
Karo na 3 kenan da dakarun sojin kasar ke samun nasarar dakile shirin satar mutane a Kaduna a cikin sa’o’i 48.