Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, ta ce an kwato jaririn tagwayen mai kwanaki 14 da aka sace a asibitin a Bauchi.
Dokta Haruna Liman, Shugaban Kwamitin ba da shawarar likitoci (CMAC) na asibitin ya bayyana haka, a lokacin da yake mika jaririn ga mahaifiyar ranar Talatar nan a Bauchi.
Ya ce an sace jaririn daga hannun mahaifiyar a asibiti bayan kwana takwas da haihuwarsa.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, “An sace jaririn ne a ranar 21 ga watan Satumba, 2022 da karfe 4:30 na yamma daga mahaifiyar da ke karbar magani a asibiti.”
“An ceto yaron a yau, 27 ga watan Satumba da misalin karfe 1:00 na dare cikin koshin lafiya.”
KARANTA KUMA: Wata Mata Ta Zama Ma’aikaciya Ta Sace Jariri A Asibitin Koyarwa
“Muna godiya ga Allah da kokarin da jami’an tsaron cikin gida na asibitin, da hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi wajen ceto jaririn,” inji shi.
Dakta Liman ya ce tuni jami’an tsaro suka cafke wata mata da ake zargi da kitsa wannan aika-aikar.
“A halin yanzu ana yi mata tambayoyi, abin da muka sani kenan bayan jami’an tsaro sun mika jaririn ga Hukumar Kula da Asibiti.”
“Yanzu muna mika tagwayen yaron mako biyu ga mahaifiyar fa danginsa cikin koshin lafiya.”
Shugaban ya bayyana cewa hukumar za ta yi nazari kan tsarin tsaro na asibitin tare da sanya karin na’urorin fasahar don tsaro a asibitin.
Hakimin Bauchi, Alhaji Nura Jumba, ya bukaci mahukuntan asibitin da su sake duba tsarin tsaro na asibitin domin gujewa sake aukuwar irin haka.
Ya yi alkawarin cewa shugabannin gargajiya za su rika wayar da kan al’umma kan lokutan da suka dace na ziyartar marasa lafiya a asibiti.
Jumba ya bukaci hukumar da ta kulla alaka da iyali, da nufin samun fahimtar juna.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Da yake mayar da martani a madadin iyalan jaririn, Malam Shitu Kalid ya bayyana jin dadinsa ga mahukuntan asibitin bisa damuwar da suka nuna da kuma jami’an tsaro kan ceto jaririn. (NAN)
A wani labarin kuma: Rundunar Yan Sanda Ta Ceto Mutane 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Uyo
Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kubutar da mutane biyar daga sansanin wasu mashahuran masu garkuwa da mutane biyu.
An ce masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da wata motar bas ta Power Link Transit Company dake jigilar fasinjoji daga Fatakwal zuwa Uyo, inda suka yi awon gaba da biyar daga cikinsu.