Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce an ceto mutane 9 daga wani gini da ya rushe a yankin Maryland da ke Legas a ranar Litinin din nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ko’odinetan yankin Legas na hukumar Ibrahim Farinloye ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya baiwa a gidan talabijin na Channels.
Ya ce, “NEMA ta samu sanarwar damuwa a wani bene da ya rushe, inda aka ce mutane tara sun makale. Ginin yana kan titin Akinwunmi 47, Akinwunmi North, a Estate Mende, da ke Maryland, a Ikeja.”
“An yi nasarar ceto dukkan mata tara da suka makale,” in ji shi.
Karanta kuma: Kwamishina Ya Yi Murabus Saboda Rushewar Gini
Jami’in hukumar ta NEMA ya ruwaito daya daga cikin wadanda aka ceto mai suna Ms Blessing ta ce wadanda abin ya shafa mata ne.
Farinloye ya bayyana cewa “mai gidan ya yi amfani da tsani don tserewa amma NEMA ta tambaye shi kan rashin tuntubar masu bayar da agajin gaggawa maimakon daya daga cikin ofishin wanda abin ya shafa ya tuntubi hukumar”.
Ya ce: “Maigidan ya zo wurin da lamarin ya faru, kuma an mika shi ga ‘yan sanda saboda ya bar mata masu rauni. Kimanin gine-gine 35 a Estate Akinwumi, gine-gine 31 a Estate Arowojobe, da Ebun Otti Estate sun lalace”.
Sauran hukumomin da suke wurin sun hada da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA); Hukumar kashe gobara ta Jiha, da sashin kula da bala’i na ‘yan sanda.
Ruwan saman da aka yi da sanyin safiya, wanda ya dauki kimanin sa’o’i hudu, ya haddasa ambaliya a yawancin al’ummar Legas.
A wani labarin kuma: 2023: Za Mu Aike Da Atiku Gidan Ritayarsa A Dubai, Inji Shettima
Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya bayyana Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, a matsayin da siyasar yawon bude ido da ke barin kasar nan zuwa Dubai, hadaddiyar daular larabawa don yawon shakatawa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tsohon gwamnan jihar Borno ya ce idan har kyakkyawan tarihin bayar da hidima, jagoranci nagari da kuma iya daukar ƙwararrun masu gudanar da mulki sun kasance ma’auni, Atiku ba zai iya daidaita kansa da Asiwaju Bola Tinubu, ɗan takarar APC ba.