Jami’an ‘yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 45 a duniya da kawunsa ya ɗaure shi tsawon shekaru 15 bisa zargin taɓin hankali a jihar Sokoto.
An ceto Salisu Muhamamd ne a ƙauyen Gidan Madi da ke ƙaramar hukumar Tangaza, bayan maƙwabta sun kai wa gwamnati ƙara.
Mai ba Gwamna Aminu Waziri Tambuwal shawara kan kare hakkin Ɗan Adam da hukumomin Agaji, Hajiya Ubaida Bello ta ce maƙwabta ne suka kai ƙara game da halin da Salisu ke ciki.
“Maƙwabtan sun zaci mutumin da kawun nasa ya ɗaure ya daɗe da rasuwa saboda sun fi shekara 10 rabon da su gan shi; da suka gano halin da yake ciki sai suka yi gaggawar sanar da mu.
“Hakan ce ta sa muka yi wa gidan tsinke tare da ‘yan sanda da masu kare hakkin Ɗan Adam da jami’an ƙaramar hukumar, har da shugaban karamar hukumar, muka ƙwato shi”, kamar yadda Ubaida ta bayyana.
Ta ce sun iske mata biyu a gidan ciki har da ɗiyar wanda aka ɗaure ɗin mai shekara 19 da ta ce ba ta san iya tsawon lokacin da mahaifin nata ke a ɗaure ba.
“Mun same shi cikin mawuyacin hali. A wurin yake fitsari da bayan gida ba tare da samun wata kulawa ba.