A halin yanzu ana ci gaba da jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Ana gudanar da jana’izar Sarauniyar wacce ita ce sarki mafi dadewa a kan karagar mulki a birnin Landan.
Ta rasu ne a ranar 8 ga watan Satumba tana da shekaru 96, wanda ya bar mutane da yawa da yin jimamin rasuwarta duk da cewa mutane da yawa suna tunanin rayuwarta da irin rawar da ta taka a matsayin Sarauniya, ba kawai ta Burtaniya ba har ma a duniya.
KARANTA KUMA: Elizabeth Ta Taimakawa Najeriya A Lokacin Yakin basasa
Bayan rasuwarta, an nada Sarki Charles III, a wata rana, tare da sauran dangin sarauta da shugabanni daga sassan duniya domin gudanar da jana’izar.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, Karatun Littafi Mai Tsarki, addu’o’i da rera waƙoƙin yabo sun riga sun fara, kamar yadda Sarauniyar ta yi tafi gidanta na karshe.
A wani labarin kuma: Majalisar Wakilai Za Ta Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki Da Shugabannin ASUU
Majalisar Wakilai za ta gana da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita mai dorewa kan yajin aikin da kungiyar ta shiga.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Yahaya Danzaria ya fitar ranar Litinin din nan a Abuja.