Labaran dake fitowa daga shafin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ya tabbatar da cewar an cimma yarjejeniya tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda biyu wato Real Madrid dake ƙasar Andalus da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham dake ƙasar Ingila.
Inda suka cimma yarjejeniya akan matashin ɗan wasan Real Madrid wato Sergio Ruguilon inda Tottenham ta saye shi akan kuɗin da suka kai kimanin £27m kuma anasa ran za’a kammala duba lafiyarsa a wannan yammaci na Laraba.
Tun a makon daya gabata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta fara maganar sayen ɗan wasan duba da yadda mai tsaron gidan Manchester United wato David De Gea ya saka hotonsa tare da Reguilon a shafin Instagram sannan ya rubuta cewar ya kamata yaron ya dawo Manchester United.
Bayan cimma yarjejeniyar ɗan wasan ya amince zai sanya kwantaragin shekaru biyar wato daga yanzu zuwa shekarar 2025 tare da ƙungiyar ta Tottenham da ake kira da fararen balbelu.
Shidai wannan matashin ɗan wasan yana a matsayin aro a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla inda da taimakonsa suka lashe gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai wato Europa League bayan da suka sha da kyar a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan dake ƙasar Italia daci 3 da 2.