Mafarkin mai tsaron gidan Manchester United Dean Henderson na buga gasar Euro 2020 ya gamu da cikas, bayan da aka cire sunansa daga jerin yan wasan gasar, biyo bayan rauni sa ya samu.
Mai tsaron gidan wanda ya girma a Old Trafford, bai kasance cikin jerin yan wasan Ingila da suka fafata da Croatia ba ranar Lahadi.
Yanzu haka wannan rauni ya tilasta dan wasan komawa Old Trafford don karɓar jinya, lamarin da ake gani ya bankwana da gasar kenan ta bana.
Yanzu haka an maye gurbin Henderson da Aaron Ramsdale inda zai ci gaba da jan zarensa.
Comments 1