Ɗaya daga cikin muhimman dokokin yin ƙwalliya shine yin amfani da launikan da suka dace da launin fatar jiki. Sai dai a yanda alamu ke nunawa ba kowa bane yake son bin doka.
Wata budurwa ta ɗauki hankula a yanar gizo inda mutane su kayi ta mata dariya bayan bayyanar bidiyon wata iriyar kwalliya da aka yi mata. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Wasu abubuwa 2 da dole sai Arsenal tayi kafin ta samu nasarar lashe gasar Premier
A cikin bidiyon an nuno ta tana ta murmushi yayin da ake ɗaukarta, inda take sanye da wasu kaya masu launin ruwan ƙasa.
Sai dai, abinda yafi ɗaukar hankali shine yanayin kwalliyar da aka yi mata wacce kwata-kwata ba tayi kyau.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan kwalliyar da aka yi mata, inda da dama suka bayyana inda aka samu matsala har ba tayi kyau ba.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda jaridar Dimokuraɗiyya ta tattaro:
foz_ay ta rubuta:
“Yanzu wacce take ɗaukar bidiyon tayi kamar bata lura cewa an damɓara kwalliyar ba? Irin mutanen da yakamata ka watsar kenan. Hakan bai dace ba.”
chinonysconcept ya rubuta:
“Na fahimce cewa akwai al’adun da suke yin kwalliyar su a haka. Don haka ya danganta daga ina wannan ta fito.”
she_is_a_scorpio ta rubuta:
“Wane laifi ta yiwa mai yin kwalliyar nan ne?”
serwaa___akoto ta rubuta:
“Kwalliyar tayi an dai cika damɓarawa ne kawai.”
birkins_n_wine ta rubuta:
“Damɓarawar ne kawai matsala, amma kwalliyar tayi kyau.”
Bidiyon bikin ƴar shekara 57 mai kama da tsaleliyar budurwa ya ɗauki hankula
Wata kyakkyawar mata mai shekara 57 a duniya, ta auri abin ƙaunarta tana sanye da wata rigar amare mai launin ja.
Matar ta sanya wani ɗan gajeran bidiyo a TikTok, wanda ya nuna lokacin da ta iso wajen taron bikin. Bidiyon da yanzu haka sama da mutum miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu suka kalla.
Mahafinta mai shekara 80 a duniya shine ya rakota zuwa wajen bikin. Dattijon sam bai yi kama da shekarun sa, inda kamanninsa suke kamar na wani mai sauran jini a jika.