Hukumar yaki da shan kwayoyin karin kuzari ta haramtawa mai tsaron ragar kungiyar Ajax dan asalin kasar Kamaru Anddre Onana buga wasanni da tsawon shekara guda.
Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta Ajax tace gwaji ne ya gano tasirin kwayoyin karin kuzarin a jikin Onana.
Sai dai tace daga bisani bincike ya nuna mai tsaron ragar tata, ya kyankyami maganin Furosemide mallakin matarsa ne a bisa kuskure, bayan fama da masassara a ranar 30 ga watan Oktoba, wanda ke cikin kwayoyin da aka haramtawa ‘yan wasa.
A kokarin ta na nemawa mai tsaron ragar tata sassauci, Ajax ta ce hatta hukumar UEFA na da tabbacin cewar Abdre Onana bai kurbi maganin Furosemide da nufin ha’inci ba, da haka za ta kalubalanci hukuncin dakatar dashi daga buga wasanni na tsawon shekara guda ta hanyar daukaka kara.