By Ishaq Dabai
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye Luka Zhekaba, bisa zarginsa da hannu wajen aikin bogi na daukar malaman sakandare 38 a jihar.
Kakakin majalissar dokokin brahim Abdullahi, shine wanda ya sanar da dakatarwar yayin gudanar da zaman majalisar a ranar Litinin.
Dakatar da Zhekaba ta zo ne biyo bayan da majalisar ta tattauna kan batun rahoton daukar malamai guda 366 bayan da aka samu malaman bogi guda 38 da ake biyan su albashi a matsayin ma’aikatan jihar.
Kakakin majalissar ya ce “Kwamitin ya ba da shawarar da a dakatar da Hon Luka Iliya Zhekaba, mataimakin shugaban marasa rinjaye na gidan tare da kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki zarginsa da ake da hannu a aikin dauka makamai na bogi.”
“Daga nan na kafa kwamitin wucin gadi na maza uku don gudanar da bincike kan zargin da ake yi masa sannan ya dawo gidan cikin makonni biyu.
“Hon. Suleiman Yakubu Azara, mamba mai wakiltar mazabar Awe ta kudu shine zai zama shugaban kwamitin; Hon. Usman Shafa, mamba mai wakiltar mazabar Toto/ Gadabuke, da Hon. Samuel Tsebe, mamba mai wakiltar Akwanga ta kudu za suyi aiki a matsayin membobin kwamitin na wucin gadi.
“Yayin da Mista Ibrahim Musa, mataimakin magatakardan majalissar shine sakataren kwamitin
A saboda haka zan iya tambayar ayyukansa ko shigarsa ba a yanzu har sai kwamitin ya kammala bincikensa. ”
Abdullahi ya ce gidan bai sabawa daukar malaman aiki ba amma dole ne a bi tsarin da ya dace don yin adalci, ya kara da cewa daukar malaman ya zama aikin lokaci -lokaci ne.
Mai magana da yawun ya bukaci mahukuntan Hukumar Kula da Malamai ta Jihar TSC da su kula da nauyin da ya rataya a wuyansu don amfanin bangaren ilimi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan ayyukan MDAs don tsabtace tsarin.
Comments 1