An soke dukkanin tashin jiragen sama na haya a birnin Kabul na kasar Afghanistan, kamar yadda hukumar kula da tashi da saukar jiragen sama na kasar ta sanar, a safiyar yau Litinin.
“Dukkannin filayen saukan girajen dake Kabul an dakatar da su cak na wucin gadi, Kuma tuni aka shaida wa Fasinjoji da kadda su halarci wurin, har sai an sake fitar da wata sanar wa” inji sanar war.
Hana tashin jiragen na zuwa ne bayan da yan Taliban, su ka kutsa birnin Kabul a jiya Lahadi, ya yin da daruruwan yan kasar suka fara yin kaura zuwa wasu wuraren sabida firgici.
KARANTA WANNAN LABARIN: Auren Zahra Diamond da cire Ummi Rahab, meye makomar Fim din Farin Wata?
Hukumar sauka da tashin jiragen samar kasar, a cikin sanar war ta bayyana cewa, ta dau wannan matakin ne, kafin al’amura su dai-dai-ta a kasar.
Kazalika Hukumar ta kuma ce, “Ta na bakin kokarin ta na ganin cewa, komai ya dai-dai-ta, nan bada jima wa ba” a cewar sanar war.
Sai dai a wani labarin kuma da kungiyar Taliban ta fitar, ya nuna cewa, ta tabbatar wa da mazauna birnin Kabul cewa, zasu sami cikakken kula wa na rayukar su, da kuma dukiyoyin su.
Comments 1