An damƙe manyan ƴan bindiga dake Oyo.
Ƙungiyar Ametokun dake kula da harkokin tsaro a Oyo sun sanar da damƙe gawurtattun ƴan bindiga dake damun yankin.
Ametokun sun sanar da labarin ne a kafar sada zumuntarsu inda suka ce an damƙe ƴan bindigan ne tare da bindiga kirar AK47 da harsashi da dama.
Ƴan ta’addan sune mai suna Muminu Salie mai shekaru 45 da biyar da Ibrahim Suleiman mai shekaru 25.
An cafke Ƴan bindigan ne a ƙauye Alapa Lanlate dake karamar hukumar Ebarapa.