Gwamnatin jihar Edo ta tabbatar da cafke wasu Dagatan kauyuka biyu kan harin da aka kai a tashar jirgin kasa ta Igueben a ranar 7 ga watan Janairu.
Chris Nehikhare, kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta jiha a Benin ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsawon Shekaru 24 Ana Tafka Kuskure, Zaben Kuskure Ya Kawo Nijeriya Inda Ta Ke – Kwankwaso
Ana tsare da wasu mutane bakwai da ake zargi, yayin da sauran fasinjoji biyu da ke hannun masu garkuwa inda jami’an tsaro suka ceto su.
Mutanen biyu ma’aikatan Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ne.
“Labarin nasara shine an kama mutane biyar da wasu sarakunan gargajiya wato Dagatan kauyyuka biyu dangane da lamarin kuma suna taimakawa da bincike,” in ji Nehikhare.
Dangane da bullar cutar zazzabin Lassa, ya ce Gwamnatin Tarayya da hukumominta sun gaza wajen bayar da tallafi ga Edo duk da kiraye-kirayen neman agaji.
“Sama da mutane 50 sun kamu da zazzabin Lassa. Muna da adadin mace-macen kashi biyar cikin dari wanda ya yi yawa idan aka kwatanta da COVID-19.”
Nehikhare ya ce Gwamnatin Edo ta tuntubi Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran hukumomin kasa da kasa domin neman taimako.
Ya ce an rubuta wasiku zuwa ga ma’aikatar lafiya, NCDC da sauran hukumomi “amma abin takaici sun ki kawo mana agaji”.
A wani labarin kuma, Gwamnan Kudu Ya Gana Da ‘Yan Takarar APC Yana Tsaka Da Rashin Lafiya
Duk da cewa yana cikin rashin koshin lafiya, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a ranar Talata ya gana da daukacin ‘yan takarar jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, gabanin zabe mai zuwa.
Gwamnan wanda ya bayyana a wajen taron cewa za a fara yakin neman zaben Sanata na jam’iyyar a mako mai zuwa, ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar da su yi aiki tukuru da kuma zage damtse domin gudanar da zabe mai zuwa.