Akalla ‘yan Najeriya 150 ne a jiya aka dawo da su gida daga Yamai na Jamhuriyar Nijar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tarbe su a filin sauka da tashin jiragen sama na Kasa da kasa na Murtala Muhammed International Airport (MMIA), da ke Legas.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Wadanda suka dawo don radin kansu sun iso ne a cikin wani jirgin sama kirar Boeing 737-4B7 na Sky Mali mai lamba FMI 6001 wanda ya sauka a tashar Cargo Wing na filin jirgin saman Murtala Muhammad da misalin karfe 11:20 na dare.
KARANTA HAKANAN Rashin Sabbin Kudi Yasa Yan Najeriya Amfani Da kudin Nijar
Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM ce ta dauki nauyin dawo da ‘yan gudun hijira daga Nijar.
Ko’odinetan hukumar NEMA reshen jihar Legas Ibrahim Farinloye wanda ya wakilci babban darakta Alhaji Mustapha Ahmed ya tarbi mutanen da suka dawo tare da sauran hukumomin gwamnati.
Wadanda aka dawo da su sun hada da manya maza 98, yara maza 11 da jarirai maza biyu yayin da akwai manya mata 24, yara mata 13 da jarirai mata biyu.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa, Sauran hukumomin da suka shiga aikin sun hada da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), NAPTIP, FAAN, ‘Yan sandan Najeriya da kuma Hukumar Kula da Lafiya ta tsandauri ta Najeriya.
A Wani Labarin Kuma Ba Mu Bijirewa Hukuncin Kotun Koli Akan Kudin Naira Ba – Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da maganar cewa gwamnatin tarayya ko babban bankin Kasa (CBN) ta ki amincewa da wasu tsofaffin takardun kudi na Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira 1,000 duk da hukuncin kotun koli.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Zamfara, Kaduna da Kogi sun garzaya kotun kolin Najeriya domin neman agaji a madadin ‘yan kasar domin kalubalantar ranar 10 ga watan Fabrairu, CBN na daina amfani da tsofaffin takardun kudin Naira da ya yi.