Wasannin masu buƙata ta musamman wasa ne da aka warewa guragu da sauran masu nakasa da suke fafatashi daga lokaci zuwa lokaci inda suma akwai kakar wasa tasu ta daban a nan Najeriya da sukeyi duk shekara.
A yammacin jiya dai an fafata wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta masu buƙata ta musamman ta Kano Pillars da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta masu buƙata ta musamman ta jahar Sokoto inda Kano ta lallasa Sokoto daci 7 da nema a wasan da suka fafata a yammacin jiya a babban birnin tarayya Abuja.
Wannan kakar wasan ta 2020 zuwa 2021 itace kakar wasa karo ta 8 kenan bayan da akayi kakar wasa har guda 7 a baya. Wannan wasa na masu buƙata ta musamman wasa ne da yake nuni da cewar suma nakasassu ba a barsu a baya ba wajen harkokin wasanni kuma wasa ne dayake ƙaramusu karsashi.