Tuni aka fara fafata gasar ƙwallon rairayi karo na farko a jahar Taraba wato jiya kenan 16 ga watan Satumba na shekarar nan da ake ciki ta 2020 wato a Arewa maso gabashin ƙasar nan ta Najeriya kenan.
Jonah Adamu wanda yayi mataimakin mai horas wa ta ƙwallon rairayi ta ƙungiyar ƙwallon rairayi ta Nigeria Customs Service ta mata har sau biyu shine ya assasa wannan gasa kuma shima tsohon gogaggen mai fafata ƙwallon rairayi ne.
A tattaunawar da jaridar www.dimokuradiyya.com.ng tayi dashi ya bayyana cewar sun sanya wannan gasa ne domin zaburar da matasan ‘yan wasa na ƙwallon rairayi musamman a Arewa maso gabashin ƙasar nan inda a nan gaba za a ƙyaƙyashi ‘yan wasan daza su baiwa mara ɗa kunya.
Sannan Jonah Adamu ya bayyana cewar a Arewa maso yammacin ƙasar nan akwai matasan ‘yan wasan ƙwallon rairayi masu basira da hazaƙa wa ‘yanda a nan gaba za ayi alhfahari dasu a ƙasar nan ta Najeriya musamman wajen wakiltar ƙasar nan a wasannin gasar ƙwallon ta rairayi.
Bayan anyi bikin buɗe gasar a yammacin jiya inda za a kwashe kwanaki 3 ana fafata gasar wato daga ranar 16 ga watan nan na Satumba zuwa ranar 19 ga watan Satumba.