Ayanzu haka an fitar da jerin ‘yan takarar lashe gwarzon matashin ɗanwasa na shekarar da ake ciki ta 2020 duba da yadda ake da gwarazan matasan ‘yan wasa a halin yanzu kuma masu basira da hazaƙa musamman a wannan shekarar ta 2020.
An fitar da jerin ‘yan wasanne a wannan rana ta Alhamis kuma daga cikinsu ne za a zaɓi wanda zaizamo gwarzo wato ya lashe wannan kyauta ta gwarzon matashin ɗan wasa.
Ita dai wannan kyauta ba kowanne ɗan wasa ne yake samun damar lashetaba hanin cewar idan wata shekarar ta dawo shekarunsu daɗuwa sukeyi kuma sai shekarar-shekara ake bayar da wannan kyautar.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan da aka fitar domin yin takarar lashe gwarzon matashin ɗan wasan na shekarar 2020:
The 2020 Golden Boy shortlist:
Bakker.
Camavinga.
David.
Davies.
Dest.
Fabio Silva.
Ansu Fati.
Foden.
Gravenberch.
Greenwood.
Haaland.
Hudson-Odoi.
Kulusevski.
Rodrygo.
Saka.
Jadon Sancho.
Szoboszlai.
Tonali.
Ferran Torres.
Vinicius.
Shin ko wanne ɗan wasa ne zai lashe wannan kyauta ganin cewar kusan kowanne ludayinsa yana kan dawo a wannan lokacin? kawai dai lokaci ne zai nuna idan anyi zaɓen.