An fitar da yadda rukunin gasar ƙwallon kwando mai taken Basketball Championship wadda akayiwa laƙabi da Rilwanu Idris Malikawa Garu mataimakin shugaban marubuta labaran wasanni na ƙasa na Arewa maso yammacin ƙasar nan.
Inda aka fitar da rukunin A dana B.
Rukunin A
Bukavu Blinks.
Paki Warriors.
Young Stars.
Ahmadiyya College.
Rukunin B.
Fiat Thunders.
K/Mata Dragons.
Kabuga Warriors.
T/Wada Warriors
Za a fara wasan a ranar 16 ga wannan watan inda za a fara fafata wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon kwando ta Bukavu da Paki.
Sai kuma a fafata wasa na biyu tsakanin Fiat da
Ƙofar Mata.
Za a fafata dukkanin wasannin da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da sauran wasannin a ranakun Alhamis da Juma’a sannan kuma za a fafata wasan ƙarshe a ranar 19 ga watan nan na Satumba.
Za a dinga fafata wasannin a filayen wasan ƙwallon kwando na Rumfa Collage dake jahar Kano.