Kyautar gwarzon ɗan wasan wata na gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila kyauta ce da ake bayar da ita duk wata d zarar an fara fafata gasar ta Firimiya, inda ake amfani da gudun mawar da kowanne ɗan wasa ya bayar sannan kuma da yin ƙididdiga akan irin wasannin da ƙungiyar da kake bugawa wasa gudanawa ta lashe a watan, shin tayi nasara duka kokuwa harda kunnen doki kokuwa ta sami nasara akan wasu wasannin kokuwa lasheta akayi duka wasannin data buga.
Tuni a sabuwar kakar wasan gasar ajin Firimiya ta Ingila aka shiga mako na uku kuma a wannan ƙarshen makon za a buga wasannin mako na huɗu yayin da tuni wasu ƙungiyoyin ƙaallon ƙafar sula lashe dukkanin wasannin nasu guda uku kamar su Everton da Liverpool da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City.
Ganin cewar a halin yanzu anci watan farko da fara fafata gasar ta ajin Firimiya shine ake sa ran za a fara bayar da kyautar gwazon ɗan wasa na wata da kuma gwarzon mai horas wa na wata, idan za a iya tunawa a kakar wasan data gabata mafi akasarin kyautar ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ne sukafi lashe wa duba dayadda suka dinga yin fyaɗar kaɗanya akan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa.
Sannan haka a ɓangaren gwarzon mai horas wa saida Jurgen Klopp ya lashe wajen sau 5 ajere batare da wani mai horas wa ya lashe ba inda tarihi ne kuma ya kafa na yawan lashe wa a kakar wasa guda ɗaya da babu wani mai horas wa a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila daya taɓa yin hakan sai shin tunda aka fara bayar da kyautar. Klopp yayi wannan bajintar ne a kakar wasan data gabata inda shine ya jagoranci Liverpool ta lashe gasar ajin Firimiya a karon farko tun bayan sautamasa suna.
Tuni hukumar dake shirya gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila ta bayyana sunayen wasu ‘yan wasa da aka fitar da za suyi takarar lashe kyautar gwarzon watan Satumba na sabuwar kakar wasa da aka fara fill a leda tun a makonni guda 4 da suka gabata, sai dai abin mamaki ana zaton wuta a maƙera sai gata ta tashi a masaƙa, domin kuwa tabbas an sami sababbin fuska a jerin sunayen ‘yan wasan ciki kuma harda sababbin ‘yan wasa inda a kakar wasa ta bana suka tsallako gasar ta ajin Firimiya.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan kamar haka:
1. Patrick Bamford.
2. Dominic Calvert-Lewin.
3. Timothy Castagne.
4. Harry Kane.
5. Tariq Lamptey.
6. Sadio Mane.
7. James Rodriguez.
8. Jamie Vardy
Mafi yawan mutane tambayar da sukeyi ko wanene zai lashe wannan kyauta ganin yadda aka fitar da sunayen ‘yan wasan babu sunan wani ɗan wasa ko guda daga ƙungiyoyin Manchester City ko Manchester United ko Chelsea kokuma Arsenal, hasali ma anga sababbin sunaye daban.
Daga cikin sunayen harda sunan sabon ɗan wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta saya wato James Rodriguez wanda tun daga ranar daya fara fafata wasan gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila ya fara bayar da gudun mawa ta ban mamaki daman kamar ya jima yana buga gasar ta Firimiya, shidai James kafin zuwansa Everton ya fafata gasa a manyan gasar rukuni-rukuni a nahiyar turai wato gasar Laliga da gasar Bundes Liga kuma ya fafata wasansa ne a manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa kamar su Real Madrid da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich.