Jami’an tsaro sun kaddamar da bincike game da wata gawa da aka binciko a gidan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mohammad Elneny, don gano musababbin samun gawar a gidan, inji rahoton jaridar Blue Print.
Wata Majiya mai tushe ta ruwaito cewa an gano gawar ne a wani sabon gida da Elneny ke ginawa a birnin Mahalla El Kubra na kasar Misra, don haka dan kwallon baya zama a gidan, kuma mahaifinsa ne ya gano wannan gawa, sannan ya kai ma jami’an tsaro rahoto.