Shugaban Alkalai na Jahar Zamfara ya rantsar da sabbin masu bautar kasa dubu daya da dari takwas a garin tsafe dake Jahar Zamfara. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
An dayi bukin rantsar da masu bautar kasar ne a wani mazaunin Yan bautar kasan dake kan titin Gusau a garin Tsafe Jahar Zamfara.
Shugaban Alkalan na Jahar Zamfara, Kulu Aliyu, ya yaba da irin ayyukan da matasa masu bautar kasa keyi, inda ya shawarci wadannan sabbin da su zage damtse wajan gudanar da ayyukan tallafawa kasar.
KARANTA:- Hatsarin mota: FRSC tace anyi hadura 5,320, inda 2,471 suka rasa rayukansu a cikin wata shida
Shugaban kotun Majistret, wadda Lubabatu Aliyu Kanoma, ta wakilta, ya shawarci matasan da su zama masu kyakykyawan dabi’a, su kasance wakilai ne na jahohin su a duk inda suka sami kansu.
Sai dai Kodineta na masu bautar kasar na Jahar Zamfara, Muhammad Namallam Taura, ya taya matasan murna domin samun nasarar kammala karatunsu na jami’a ba tare da matsala ba.
KARANTA:- Saboda tsabar kyan da Allah Ya mun ya sa na tsani kwalliya, Cewar Ummi Zee-zee
Namalam Taura, ya cigaba da cewa abunda ake nufi da masu bautar kasar, wata dama ce da matasa ke dashi wajan bada gudunmawar su ta yadda za’a ciyar da wannan kasar gaba, musamman ma nan Jahar Zamfara.
Muna fatan zaku bada gudunmawar sosai wajan kawo cigaba a Jahar ta Zamfara.
Ya Kuma janyo hankalin matasan dasu kasance sun bada gudunmawar su, suna shiga duk wani aiki da ya shafe su.
Namallam Taura, ya yabawa shuwagabanni da jagororin matasan baki daya na jahar Zamfara.
Ya kuma shawarce su da su cigaba da tallafawa kada su gaji har karshe.
a yayin gudanar da rantsuwar dai an lafta wani mamakon ruwan sama.