A cigaba da gano mutanen da suka rasa rayukansu a harin da ƴan ta’adda suka kai a kudancin Kaduna, a halin yanzu an gano gawawwaki kimanin mutane 45 da suka mutu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Idan dai ba’a manta ba Kwamishinan yaɗa labaru da harkokin gida a ranar Litinin, yace kimanin mutane 34 ƴan ta’adda suka kashe a Madamai, ƙaramar hukumar Ƙaura ta jahar Kaduna.
Ya kuma ce an kashe kimanin mutane takwas a zangon-kataf, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akwai Jami’an dake taimakon ƴan ta’adda da bayanan sirri a cikin Hukumomin tsaro — Cewar Ahmed Audi
Amma a ranar Talata a cikin wani jawabi daya fitar, jim kaɗan bayan yakai ziyara a wurin da lamarin ya faru, Kwamishinan yace an samu ƙarin gawarwakin mutane 3 da jami’an tsaro suka gano.
Sanarwar mai taken ‘an gano gawarwaki ta mutane 3 a ƙananan hukumomin Ƙaura, da Zangon Kataf.
Kwamishinan yace “biyo bayan kai hari a cikin hutun mako a ƙauyukan Madamai da Kacecere na ƙananan hukumomin Ƙaura da Zangon Kataf, jami’an tsaro a ranar Talata sun gano gawar mutane 3.
“Acewar jami’an tsaro, an samu gawa biyu a Madamai, a yayinda aka samu ɗaya a Kacecere. Ana cigaba da bincike gami da gano sauran waɗanda suka ɓace, kuma gwamnati zata cigaba da sanarwa al’umma duk halin da ake ciki.