Rundunar ‘yan sandan reshen jihar Kaduna ta gano gawar wani dan Acaba mai suna Benedict Garba dan shekara 45 a kauyen Kamazou a jihar. Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar inda ya ce; an gano gawar wani matashi, Benedict Garba, mai zama a Maraba Rido a Kaduna a yayin da aka ga gawarsa a unguwar Kamazou kusa da hanyar Ibrahim Yakowa Expressway, Kaduna.
A sanarwa ya ci gaba da cewa, “an gano gawar Garba dan shekara 45 tare da wani dan Acaba da tsaga iri daya a tsakiyar kansu da fuskarsu a wannan yankin.”
A cewar Sabo a ranar 09/09/2019 da misalin karfe 09:00 na ranar, rundunar ta samu labarin daga DPO Sabon Tasha wato shugaban ofishin ‘yan sanda Sabon Tasha, inda ya bayyana ma rundunar cewa ana gano gawar wani matashi a Kamazou a ta hanyar Ibrahim Yakowa Expressway.
“An nan take ba tare da bata lokaci ba aka aika jami’an bincike zuwa inda abun ya fari domin su duba tsagen da aka yiwa mamacin. Hakan ya sa jami’ai suka kara sanin yadda abubuwa ke gudana. Daga baya aka gano cewa gawar wani matashi ne mai suna Benedict Garba mai zama a Maraba Rido wanda ya kasance mai sana’ar acaba ne. An dauke hoton gawar sannan kuma aka kai gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki wanda ke babban asibitin Sabo.” In ji shi.
Ya kara da cewa; “Rundunar na iya kokarinta wajen gano wadanda suka aikata wannan mummunar aiki, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ali Aji Janga ya bada umurnin gudanar da bincike a kan gano dalilin da ya sa aka aikata kisan. Za mu kawo ma ku ci gaban labarin da zaran mun gano wani abu game da lamarin.” Ya tabbatar.