By Abbas Yakubu Yaura
An gano gawarwakin wani fitaccen mai gidan rawa, Steven Ayika da kuma uwargidan sa, Chiamaka Emmanuel a cikin mota a jihar Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da samun gawarwakin ‘yan biyun da suka rasa rayukansu a cikin wata mota.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa DSP Haruna yace, “A ranar 11/23/2021 da misalin karfe 0450, an samu rahoton cewa an ga wata mota a kan hanyar Katsina dake karamar hukumar Fagge Jihar Kano dauke da mutane biyu (2), mace da namiji basa motsi.
“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya tashi tare da umurtar tawagar ‘yan sanda dasu ziyarci wurin da lamarin ya afku.
“Nan take tawagar ta garzaya wurin da lamarin ya faru, Inda suka Tarar da wadanda lamarin ya rutsa dasu, namiji da mace a cikin kujerar baya ta Motar Siena,nan take aka garzaya dasu Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, inda wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu.
DSP Kiyawa ya bayyana cewa, “A binciken farko, an bayyana sunan marigayin mai suna Steven Ayika, ‘m’, na Jaba Quarters Kano, yayin da matar data rasu itama suka samu bayaninan sunanta da Chiamaka Emmanuel, ‘f’, mai adireshi daya. Sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike.