An gano gawarwaki 15 a Iftila’in Ambaliyar Ruwa na Borno – NEMA
Muhammad Usman, Jami’in Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a shiyyar Arewa maso Gabas, ya ce kimanin gawawwaki 15 ne aka gano a kogin Ngadabul da ya mamaye birnin Maiduguri na jihar Borno.
Ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi al’ummomi da dama da ke gabar kogin Maiduguri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani Ya Sami Wani Tabbaci Daga Shugabannin APCn Kaduna Shiyya Ta 2
Da yake magana da Manema Labarai a Maiduguri a ranar Laraba, ya shawarci iyaye da masu kula da su da su gargadi ma’aikatansu da ‘ya’yansu game da yin iyo a cikin kogin don gudun kada su nutse.
Usman ya bayyana cewa NEMA a matsayinta na hukumar kula da bala’o’i ta kasance tana wayar da kan al’umma kan hadurran da ke tattare da ambaliya da matakan kariya.
Ya kara da cewa, “Mun yi ta ganawa da masu ruwa da tsaki daban-daban kan wayar da kan jama’a da kuma samar da kayayyakin agaji ga al’ummomin da abin ya shafa.”
Hakazalika, domin dakile al’amuran mutanen da aka nutse a ruwa, rundunar jami’an tsaron farin kaya ta Jihar Borno ta tura jami’anta a bakin kogin domin fatattakar yaran da ke zuwa rafi domin yin iyo.
A wani labarin kuma: TETFUnd Ta yi wani cika baki, tace Ƴan Najeriya sun fara morar Dakin Gwajin Covid-19 data samar
Gidauniyar Kula da Manyan Makarantu da Asusun Tallafawa Ilimi TETFUnd, ta ce aikin Rigakafin Covid-19 da ta ɗauki nauyin sa zai kasance a shirye don gwajin Asibiti na farko a watan Nuwamba 2022.
TETFund ta bayyana cewa ta hanyar bada tallafi, ƴan Najeriya sun shawo kan dogon jiran da aka saba yi na tattara samfurin Covid-19 da sakamakon su.