By Abbas Yakubu Yaura
Darakta Janar ta Hukumar Kula da ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa Farfesa Mojisola Adeyeye, a ranar Juma’a, tace hukumar ta gano wasu kwalaye na haramtattun kwayoyi da suka hada da katan 10 na Tramadol a harabar baje kolin kasuwanci dake jihar Legas.
Adeyeye, a wani taron tattaunawa da aka yi a Legas ranar Juma’a, tace an kuma kama jabun magungunan da suka haura Naira biliyan 3 a rumbun ajiyar mallakar wani Chuka Akuamia.
Sannan tace, “Jami’an hukumar bincike da tabbatar da doka ta NAFDAC da hukumar yaki da jabun magunguna da abinci mara kyau sun kai farmaki a wasu rumfunan ajiya guda biyu dake rukunin kasuwanci na TradeFair dake Legas, inda suka samu wasu kwalayen haramtattun kwayoyi da suka hada da kwali 10 na (Tramadol) mai karfin milgiram 225.
“Bugu da ƙari, katan 1,200 na haramtaccen allurar Analgin (2.5g/5ml), da kuma katan 2,200 na haramtaccen Kodin na ruwa da kuma waɗanda ake zargin na jabu ne da Azmal 500,da allurar Artemeter 534 sai fakitin 300 na Biomal, da Allurar Artesunate 188, katuna na Hydra da Black Cobra (silderzafil citrate 200mg), 198 da kuma katon na allurar Super Artesunate da sauransu,inda aka ganosu tare da kuma kwashe su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Magungunan da aka haramta da kuma na bogi a cikin rumbun ajiyar mallakar wani Chuka Akuamia, wanda har yanzu ba a boye ba, an kiyasta kudin su ya haura Naira biliyan 3,inda kuma a kwashe sama da manyan motoci 20 na kayayyakin dake damun su daga wurare biyu.sai dai kuma an adana samfuran a yanayin zafi sama da 40oc wanda yawanci zai haifar da wasu abubuwan dake aiki. “
Adeyeye ta kara da cewa, a ranar Larabar data gabata ne Hukumar ta gurfanar da wani Mista Afemefuna Udensi, mai suna Phini Pharms Limited, Onitsha, a gaban babbar kotun tarayya dake Legas bisa laifin shigo da Tramadol na bogi.