By Ishaq Dabai
An samu barkewar cutar a kusa da yankin Ireti Ayo na Ilesa, yayin da aka gano wasu ma’aurata, Eso Olasunkanmi da Eso Fisayo sun mutu bayan sun ci a cikin abincin mai dauke da cutar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin data gabata, an gano ma’auratan ba su da rai a cikin dakin su.
Duk da haka an tattara cewa ma’auratan sun ci abincin daren Juma’a amma yanayin mutuwar su mai ban mamaki bai bayyana ba tukuna.
Wani mazaunin yankin, Wale Banjo, yace babu wanda ya san abin daya same su amma an gan su da farko a ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba saboda hutun da ake yi sai kawai ganin gawarwakinsu a kayi da yamma.
Opalola ya bayyana cewa an kai gawawwakin zuwa asibiti domin gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwarsu.
“An kai gawar ma’auratan asibiti domin a binciki gawar. Sakamakon zai iya taimaka mana mu gano sirrin dake bayan mutuwarsu.ya kara da cewa “A halin yanzu, ba zan iya bayyana abin da ya kashe su ba har sai bayan kammala binciken gawar.”