An gano matattun Dabbobi a Mahautar Kano
Hukumar kula da Kayayyakin da ake ci ta Jihar Kano (KSCPC) ta gano matattun dabbobi a Abattoir na Unguwa Uku Yan Awaki da ke karamar hukumar Tarauni.
Mukaddashin Manajin Darakta, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin sa, Musbahu Yakasai ya fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nada Ni A Matsayin Ko-odinetan Matasa Na Yakin Neman Zaben Tinubu Abin Mamaki Ne – Yahaya Bello
An mika wa Hukumar bayanan game da dabbobin da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Litinin.
Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa an kawo wasu matattun awaki da raguna zuwa gidan yankar.
“Sun yi zargin cewa (dabbobi) sun riga sun mutu kafin a yanka su.
Babba-Dan’agundi ya ce, “Nan da nan ne tawagarmu ta dauki matakin damke dabbobin.
Majalisar ta gayyaci wani likitan dabbobi wanda ya tabbatar da cewa dabbobin ba su dace da cin abinci ba.
Sanarwar ta kuma sha alwashin cewa za a hukunta wadanda suka aikata laifin.
A wani labarin kuma: Buhari Ya Taya Shugaban Hukumar NDLEA Murnar Nasarar Cafke Hodar Iblis Ta Biliyan 194
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya taya shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Brig.Janar Buba Marwa (mai ritaya),murna a kan nasarar da hukumar ta samu a baya-bayan nan da ya kai ga farfasa wata kungiyar dillalan kwayoyi ta kasa da kasa tare da kwato kilogiram 1,855 na hodar iblis.
Hakan na kushe ne ta cikin wata wayar tarho da ya yi da shugaban hukumar yaki da muggan kwayoyi daga birnin New York inda yake halartar taron majalissar dinkin duniya karo na 77 (UNGA 77), shugaba Buhari ya ce labarin kame kayan ya faranta ran sa.