Wani sabon rahoto da aka fitar a wannan Laraba ya bayyana cewa, tsohon gwarzon dan kwallon duniya na Argetina, Diego Maradona ya mutu ne sakamakon cutukan da ke da nasaba da koda da hanta da kuma zuciya sabanin kwankwadon barasa da muggan kwayoyi da aka bayyana da farko.
Binciken da aka gudanar kan gawarsa, bai gano wata alamar barasa ko muggan kwayoyi tattare da marigayin ba kamar yadda mai shigar da kara na gwamnatin Argentina ya bayyana.
A ranar 25 ga watan Nuwamban da ya gabata ne, Maradona wanda ya jagoranci kasarsa wajen lashe mata kofin duniya a 1986 a Mexico, ya mutu yana da shekaru 60.
An yi wa gawarsa gwaji ne don kawar da shakkun kan musabbabin mutuwarsa.
Kodayake tsohon gwarzon kwallon duniyar ya sha fama da kwankwadon hodar iblis da baraza a lokacin rayuwarsa.