An gano wata tsohuwar mata mai shekara ɗari da hamsin a duniya, wacce har yanzu tana da kyawunta a Najeriya.
Wata matashi mai gudanar da cibiyar Joy Peters Foundation da kuma bayar da kayan jin ƙai ga marasa ƙarfi, itace ta ziyarci tsohuwar. Rahoton jaridar Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Zabe: Hukumomin Tsaro Zasu Aike Da Ma’aikata Sama Da 400,000 A Fadin Kasar – IGP
A cikin bidiyon da aka sanya a manhajar TikTok, an nuna tsohuwar mai suna Aisha zaune tare da ɗiyarta a cikin wani ɗan ƙaramin gida.
Abinda yaba mutane matuƙar mamaki shine har yanzu akwai sauran kyawunta kuma tana da jiki irin wanda ba irin na masu shekarun ta ba.
Wani abu da ya banbanta da saura kan tsohuwar shine yadda fatar jikinta take yin sheƙi gwanin ban sha’awa.
Matashiyar mai suna Joy ta ziyarci tsohuwar ne bayan ta samu labarin ta da kuma yadda take rayuwa a wajen da ba mai kyau ba.
Ta ba tsohuwar wasu kayayyakin abinci da suka haɗa da shinkafa da kayan miya.
Tsohuwar ta miƙe ta ɗan taka rawa cike da farin ciki bayan kayan sun isa gare ta.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@Cynthia ta rubuta:
“Wannan mamar zata yi kyau lokacin tana budurwa. Kalli fatar ta kamar madara.”
@Habibtykayanmata ta rubuta:
“Dan Allah a wacce jiha ce?
@Manchiee ya rubuta:
“Allah yayi miki albarka ƴar’uwa.”
@princess cee ta rubuta:
“Allah ubangiji ya albarkace ki.”
Ana Dab Da Ɗaura Musu Aure, Matashi Ya Ritsa Budurwarsa Na Cin Amanarsa a Otal
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya ritsa budurwar sa na cin amanar sa a otal ana dab da a ɗaura musu aure
Wani bidiyo da aka sanya a manhajar TikTok ya nuna lokacin da wani ɗan Najeriya, ya yiwa matar da zai auri gwaji, inda ya gano cewa ashe ƴar hannu ce.
A ranar da budurwar zata zo otal ɗin, saurayin nata yana cikin ɗakin yana jiranta inda ya tsaya a matsayin wanda zai amfani da ita ya biyata kuɗi