Wani bincike ya gano wasu Gwamnoni hudu da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP dake kokarin ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu yayi nasara a zaben 2023.
Idan dai ba a manta ba, gabanin babban taron kasa na ranar 28 ga watan Mayu, shugabannin jam’iyyar PDP sun yi watsi da zaben shugaban kasa ta hanyar jefa kuri’a a fili, duk kuwa da cewa babbar jam’iyyar adawa a kundin tsarin mulkinta ta ce za a yi zaben shugaban kasa tsakanin Arewa.
Hakan ya share fagen fitowar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023.
Tun bayan nasarar Atiku ta zama ɗan takarar shugaban kasa a PDP, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike wanda ya zo na biyu a bayan Atiku a wajen taron, yake ta fafutuka ganin an sauya salon shugabancin jam’iyyar.
KARANTA ANAN: Gombe: Mamaye Ofishinmu Neman Rigima Ne Da Nuna Karaya – PDP
Wike, wanda ya damu matuka, inda ya dora laifin rashinsa a kan cin amanar da shugabannin jam’iyyar suka yi, musamman, shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal.
Tambuwal dai shine wanda ba zato ba tsammani ya yanke shawarar janyewa Atiku tare da mara masa baya.
Tuni dai Gwamnan Jihar Riba ya yi ‘yan uwantaka da Tinubu wanda kuma ya kai ga taron Landan kwanan nan, da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP.
A wani labarin kuma: Rikicin PDP: Makinde, Fayose, Wike Da Wasu Sun Gana A Ibadan
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya gana da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP, tare da hasashen matakin da zai dauka na gaba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hakan ya biyo bayan kuri’ar amincewa da kwamitin zartarwa na kasa ya kada kan amincewa da shugabancin Sanata Iyorchia Ayu.
Wike da masu goyon bayansa sun bukaci Ayu ya yi murabus a matsayin wani sharadi na zaman lafiyar jam’iyyar.