
An garkame Dan najeriya kan yima wata yar shekara 13 fyade a Amerika
Adeyinka A. Ajose Dan Najeriya mai shekaru sittin da hudu an kaishi gidan kurkuku har tsawon shekaru sha takwas kan yima wata yarinya mai shekaru sha uku fyade.
A ranar sha bakwai ga watan Yuni ne aka yankewa Ajose Hukunci a wata Kuliya mai suna Crydon Crown Court akan laifin fyade, wannan labarin yazo ne ta kafar yada labaran Yan sandan Landan.
KARANTA:- Gwamanan Jihar Neja Sani Bello ya kaddamar da wani katafaren Asibiti da aka Gina a Kontagora
Abayama an taba damke Ajose da irin wannan lafin inda yayi da wata yarinya yar shekara sha uku daganan yarinyar ta kamu da cuta.
An tabbatar da laifin aranar 29 ga watan Yuni.
Kotun tace taji cewar a misalin karfe tara da minti sha uku ne na ranar goma ga watan Nuwambar shekarar 2020 aka kira Yan sanda daga Crydon.
Bayan zuwan Yan sanda sai Yarinyar take basu bayani kan yadda lamarin ya auku, wanda tun da dadewa ansha kawo kararsa kan keta haddin yara.
Jami’an suka ce da badin Yarinyar ta sami kwarin guiwar sanar da hukuma ba da ba’a kawo karshen ta’adin Ajose ba, sannan matsalar da yasa Yarinyar zai kasance tare da ita ne har abada da ita da ahalinta.
Jami’an suka ce ” suna yabama Yarinyar kan irin kokarin da tayi tun da’aka fara bincike har aka gama”