Daruruwan al’umma ne suka halarci bikin nadin Sarkin Kanurin kasar Ghana, wanda ya gudana a yau Asabar, taron dai ya samu halartar Manya Manyan Mutane Wanda suka hada da babban limamin kasar Alhaji Usman Nuhu Sharubutu, da Mataimakin Shugaban Yan sandar kasar Alhaji Sarki Baba, da kuma Jakadan Najeriya a kasar Alhaji Hamza Shu’aibu, hadi Manya Manyan Masu kudin kasar.
Taron da aka gudanar a karamin filin wasa (Mini Studium) dake Fadama, ya samu halartar Kabilu da dama, hadi da Saraku nan su, Bayan nan kuma an gabatar da tarihin Kanuri tun daga Kanun Borno Empire har zuwa Yau.
Yayin taron masu gabatar da jawabi sun yi amfani da wannan damar wajen kira ga Iyaye da su nunawa ya’yan su Muhamancin Karatu Wanda ta haka ya’yan nasu zasu san Tarihin su.
Mataimakin Shugaban yan sanda na kasar Ghana, yayi kira ga Malaman addinai da iyaye da su kula da zirga zirgar yaran su, da kuma batun shaye shaye wadda ta zama matsala tsakanin matasan yanxu, yayin da wasu da yawa daga cikin su suke daukan hakan da sunan Ado.