Rahotanni sun bayyana cewa likitoci a asibitin koyarwa na malam Aminu Kano sun gudanar da tiyatar aikin laka a asibitin wanda kuma suka samu cikakkiyar nasara.
An rawaito cewa babban likitan daya jagoranci gudanar da aikin kuma likitan kwakwalwa Musabahu Ahmad yace sun samu nasarar gudanar da tiyatar ne bayan da wani dan kishin kasa ya samar musu da cikkakkun kayan aikin gudanar da tiyatar kuma na zamani a shekarar data gabata.
Inda ya kara da cewa wanda aka yiwa aikin masana kiwon lafiya ne suka turo shi asibitin koyarwar tun a shekarar data gabata sakamakon matsalar da ya fara fuskanta da lakar tasa.
Daga nan sai babban likitan ya bayyana godiyarsa ga Allah madaukaki bisa damar da ya basu na gudanar da tiyatar cikin nasara a asibitin na Malam Aminu kano.