By Abbas Yakubu Yaura
Wani dalibin sashin koyon aikin Jaridar na jami’ar Adekunle Ajasin mallakin gwamnatin jihar Ondo, Akungba Akoko, Ayodeji Fadare, ya gurfana a gaban wata kotun majistare dake Akure bisa zarginsa da damfarar mutane biyar daban-daban na tsabar kudi naira 486,000 na biyan kudin makaranta.
Fadare, mai shekaru 26, an ce ma’aikacin wurin sadarwar kafe ne da ake zargin ya aikata laifukan ne a shekarar da ta gabata a cikin watan Maris da misalin karfe 10 na safe daura da ofishin INEC, Alagbaka a gundumar Akure.
Dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Nelson Akintimehin ya shaida wa kotun cewa dalibin mai matakin karatu na 300 ya aikata damfara tare da canza kudin wadanda abin ya shafa har Naira 486,000 bisa zargin taimaka musu wajen biyawa ‘ya’yansu kudin makaranta.
An ce Fadare ya karbi Naira 75,500 daga hannun Omoteji Israel ta hanyar asusun ajiyarsa na banki mai lamba 0175044918 da ke zaune tare da Bankin GT a matsayin wani ma’aikacin Cyber Café a karkashin zargin taimaka masa wajen biyan kudin makarantarsa da sanin cewa karya ne.
Akintimehin ya yi nuni da cewa wanda ake tuhumar ya kuma canza kudi naira 150,000 da wata Eunice Bamidele wanda ta biya ta asusun ajiyarsa na banki mai lamba 0175044918 dake zaune a Bankin GT tare da neman biyawa diyarta kudin makaranta.
Ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya karbi karin wasu kudaden naira 155,000 daga hannun wani Gbenga Adebayo da kuma naira 55,000 daga hannun Esther Oluwatoki a matsayin wai zai taimaka musu wajen biyaws ‘ya’yansu kudin makaranta.
Mai gabatar da kara ya ci gaba da cewa Fadare ya Gudanar da damfara ya samu kuma ya canza kudi naira 51,000 daga hannun wani Oyinbodunmi Ibikunle da laifin taimaka masa wajen biyan kudin makarantar dansa.
Laifukan da ake tuhumar sa dashi sun ci karo da sashe na 418, 419, 383, 390 (9), 465, 467, da 338 na kundin laifuffuka, 37, 1, na dokokin Jihar Ondo ta Najeriya, shekarar 2006.
Sannan ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa na laifuka goma sha biyu na zamba.
Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, Mista Bernard Godwin, ya roki kotun da ta bayar da belin wanda ake tuhuma a mafi saukin sharadi.
Godwin ya yi alkawarin cewa wanda yake karewa ba zai yi tsallake sharadin bada belin ba amma ya samar da amintattun mutane.
Alkalin kotun, Musa Al-Yunnus ya bayar da belin wanda ake tuhuma a kan kudi Naira 500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Al-Yunnus ya kara da cewa dole ne wadanda za su tsaya masa su rantse da wata takardar shaida, kuma su kasance cikin hurumin kotun.
Sannan ya ce dole ne su kuma samar da takardar shaidar biyan haraji na shekaru uku tare da samar da hotunan fasfo guda biyu na baya-bayan nan.
Daga nan alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 28 ga watan Junairu, 2022 domin sauraren karar.