Daga Umar Ahamad, Gombe
An gurfanar da shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar gwambe da wasu mutane uku a gaban kotu 3 bisa laifin sama da fadi da naira miliyan 25
Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta’anati wato EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar gwambe Malam Atiku Mu’azu Bayum da wasu manyan ma’aikatan hukumar guda uku a gaban kotu bisa zarginsu da wawure wasu kudade daga asusun gwamnatin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin hukumar reshen jihar gwambe Malam Bello Bajoga ya fitar hukumar tace wadanda ake zargin sunyi amfani da matsayinsu na shugaba da mai kula da baitil mali da kuma mai kula da asusun ajiyan hukumar wajen wawure naira miliyan ashirin da biyar da naira dubu sittin mallakar gwamnatin jihar ta gwambe.
Sanarwar ta bayyana cewa; “Bincike ya bayyana wasu takardun kudade da aka fitar daga asusun hukumar don gabatar da wasu ayuka amma suka karkatar da kudaden don gudanar da bukatun kawunan su”.
Malam Bello ya kuma kara da cewa, daya daga cikin zarge zarge guda biya bayyana cewa; “Kai, Atiku Mu’azu Bayum da Mohammed Adi da Ibrahim Abubakar da kuma Abubakar Usman, a wani lokaci tsakanin watan Janairun shekarar 2014 da watan Julin shekarar 2015 a cikin garin gwambe kun hada baki don gabatar da sata wanda haka kuma laifi ne a sashi ba 96 da 97 a cikin kundin laifuffuka na dokar arewacin najeriya”.
Yayin da shi kuma zargi na biyu ya bayyana cewa; “Kai, Atiku Mu’azu Bayum da Mohammed Adi da Ibrahim Abubakar da kuma Abubakar Usman, a wani lokaci tsakanin watan Janairun shekarar 2014 da watan Julin shekarar 2015 a cikin garin gwambe kun hada baki da nufi kuka kuma karkatar da naira miliyan ashirin da biyar da naira dubu sittin (N25, 060, 000.00) mallakar gwamnatin jihar gwambe wanda yin hakan kuma laifi ne a sashi ba 286 da 287 a cikin kundin laifuffuka na dokar arewacin najeriya”.
Sanarwar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sunyi na’am da zarge zarge da hukumar ta gabatar da kawunansu, yayin da shi kuma lauyan hukumar ta EFCC O. Israel ya bukaci kotun da ta hukuntasu dai dai da laifukansu.
A jawabinsa shi kuma lauyan wadanda ake zargin L. A Haruna ya bukaci kotun da ta yiwa wadanda ake zargin sassauci, domin a cewarsa basu wahalar da shari’a ba kuma a gabanin zuwa kotun sun amince da cewa zasu dawo da kudaden.
Yayin gabatar da hukuncin shari’ar alkaliyar babbar kotun ta uku a jihar gwambe, Mai Shari’a Biatrice ta bayyana wadanda ake zargin da aikata laifuka don haka kotun ta bukaci kowannensu da biyan naira dubu dari dari a matsayin diya tare kuma da dawowa da gwamnatin kudaden da suka karkatar.