By Abbas Yakubu Yaura
Mutumin da ake zargi da hannu a tashin gobarar majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu a ranar 2 ga watan Janairu a birnin Cape Town, kan kunshin tuhumar tada gobara yayin da ya bayyana karo na biyu a wata kotu a Afirka ta Kudu a ranar Talata.
Zandile Christmas Mafe, mai shekaru 49, an kama shi ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake kan harabar majalisar kuma an gurfanar da shi bayan kwanaki uku a wata gajeriyar bayyanar da ya yi a wata kotun birnin Cape Town.
Takardar tuhume-tuhumen da ‘yan jarida suka gani, ya nuna cewa wanda ake tuhumar “yana da laifin sabawa tanadin kariya ga dimokuradiyya da ayyukan ta’addanci.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gabanin fara sauraren karar, mutane kusan 30 ne suka taru a wajen kotun domin neman a sako wanda ake zargin.” Mafe ba mai laifi bane.
Tun bayan kama shi ne dai ake ta cece-kuce a kafafen yada labarai na nuna shakku kan rawar da wanda ake zargin ke da hannu a tashin gobarar inda wasu ke zargin lamarin a kan gazawar tsaro wajen kashe gobarar.
Wani rahoto na farko ya nuna cewa tsarin gano gobara ya bayyana kuskure kuma ba a yi amfani da shi ba tun a shekarar 2017.
Indan dai za’a iya tunawa gobarar dai ta tashi ne da safiyar ranar 2 ga watan Janairu, inda ta lalata wasu sassa na harabar majalisar ciki har da majalisar dokokin kasar, wanda rufin ta ya rufta.