By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotu a Benin ta gurfanar da wadanda ake zargi da kashe mahaifiyar tsohon Gwamna Lucky Igbinedion, Mista Maria Igbinedion, Dominion Okoro, da wadanda suke da hannu a ciki a ranar Talata a gidan gyaran hali na Jihar Edo.
Wadanda ake zargin sun hada da Patience Okoro mai shekaru 39, da Francis Taga mai kimanin shekaru 51, sai Ezikiel Danjuma 24, da kuma Ibrahim Kuje.
Mai shari’a Efe Ikpomwomba ya bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari har zuwa lokacin da daraktan kararrakin jama’a na ma’aikatar shari’a ta jihar ya basu shawara.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, CSP Peter Ngwumba, ya shaida wa kotun cewa, ana tuhumar wadanda ake zargin da laifin kisan kai, mallakar kayan aikin kisan kai, sakaci, haddasa barna da fashi da sauran laifuka.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 3, da 10 zuwa 13 ga watan Disamba a Benin ta jihar Edo, da Aba ta jihar Abia; da kuma Ikom dake jihar Cross River.
Mai gabatar da kara ya kuma shaida wa kotun cewa babban wanda ake zargin, Okoro, mai dafa wa marigayiyar, a ranar 2 ga watan Disamba, a Ugbor dake GRA Benin, ya kashe ta tare da sace mata kudi naira 100,000, agogon hannu na zinare da abin wuya sannan ya gudu.
Sannan ya ce Danjuma da Kuje, wadanda ke tsaron marigayiyar ne suka bar Dominion ya tsere bayan sun aikata laifin.
Mai shari’a Ikpomwomba ya bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari, sannan ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan Janairun 2022.