By Abbas Yakubu Yaura
An gurfanar da wasu mutane uku, Sodiq Raman mai shekaru (47) da Oyetunji Oyekan (35) da kuma Akeem Balogun mai Shekaru (31), a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja, bisa laifin satar abin wuya na Naira miliyan uku.
Mutanen ukun dai sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su na hada baki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma yin sata.
Alkalin kotun, Misis R. A. Alejo, ta bayar da belin wadanda ake kara akan kudi naira miliyan 1m kowannen su tare da tsayayyun mutane biyu kowanne a matsayin wani bangare na sharuddan belin.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sgt Olasunkanmi Adejumola, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake kara da sauran su sun aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Disambar shekarar data 2021, da karfe 10 na dare a Ado Langbasa, Ajah, jihar Legas.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu.