By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne ‘yan sanda a jihar Legas suka gurfanar da wasu mutane hudu a gaban wata kotun Majistare ta Ojo, bisa zargin su da satar na’urar sanyaya daki a harabar makarantar.
Wadanda ake tuhumar dai sun hada Kpoin Weripere mai shekaru 47 da Kazeem Mutalib dan kimanin shekaru 39 sai Paul Oshoja, mai shekaru 35 da kuma Seidu Lukeman 45.
Inda suka bayyana a gaban alkalin kotun, Mista Taiwo Popoola.
Sai dai kuma sun ki amsa laifin da ake tuhumar su dashi na hada baki don yin sata.
Dan sanda mai shigar da kara, Insp Edet Ekpo, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Disamba a Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya dake Oto-Awori, Ojo, jihar Legas.
Ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne wajen sace na’urar sanyaya daki mallakar bankin UBA dake kwalejin.
A cewar mai gabatar da kara, an kama wadanda ake tuhumar ne bayan gudanar da binciken ‘yan sanda.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa laifukan da ake zargin su dashi sun sabawa tanadin sashe na 287 dana 411 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Kotun ta bayar da belin wadanda ake tuhuma a kan kudi Naira 100,000 kowannen su, tare da mutum daya da zai tsaya masu.
Kazalika Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 11 ga watan Janairun sabuwar shekara.