By Abbas Yakubu Yaura
Wata mata mai suna Fatima Sanusi da ke fuskantar shari’a bisa laifin damfarar saurayin ta Naira miliyan 10 cikin kwanaki 10 dayin bikin aurensu, ta bakin lauyanta, Barista Bala Adamu, ta shigar da kara na share fage tana kalubalantar hurumin kotu a kan lamarin.
Mahaifiyar ‘ya’ya biyu ta gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Barnawa a jihar Kaduna, bisa laifin damfarar angonta mai suna Umar Oruma, inda ta bayyana cewa ba ta da sha’awar yin auren kwanaki 10 kuma rahotanni sun ce ta aure uban ‘ya’yanta maimakon haka.
A zaman da aka koma jiya a Kaduna, Barista Adamu ya shigar da karar farko ga lauyan mai kara, Abdulbasit Suleiman.
Sai dai Barista Suleiman ya ce yana da shaidu biyar a gaban kotu, amma ya ce, “An kawo mana sanarwar kin amincewa da matakin ne da misalin karfe 9.55 na safiyar Laraba, kuma bisa ga haka, mun amince da takaitaccen lokaci da za a saurari karar farko. ”
Alkalin kotun, Aliyu Dogara, ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu, 2022.