• Ana zargin matar ne da zanba cikin aminci .
• Ta salwantar da sama da Naira milliyan guda domin biyan bukatar kanta.
• Mai shiri’ar Kotun ta bada belinta bayan ta karyata zangin da ake mata.
Rundunar yan sandan jihar Benue, ta gurfanar da wata mata mai suna Mrs Christina Lortim mai shekara talatin da takwas, a gaban wata Kotu, dake garin Makurdi, bisa zargin zanba cikin aminci.
Yar sanda me gabatar da kara Insfecta Veronica Shaagee ta bayyana wa Kotu cewa, an dawo da sauraran karar ne, daga shalkwatar yankin, zuwa sashin binciken manyan laifuffuka na Makurdi, ta cikin wata wasika mai dauke da lamba AR3100/BNS/ACM/VOL.10/14.
Shaagee tace, an shigar da karar ne ta hannu wani me suna Moses Tsegba mazaunin New Kanshio Layout, na garin Makurdi, tun a ranar 8 ga watan Mayun shekarar data gabata.
Ta kuma kara da cewa, a ranar 6 ga watan Disambar shekarar 2019, zuwa 28 ga watan Janairun shekarar 2020, Mr Tsegba ya baiwa Lortim makudan kudaden dasu ka Kai, Naira milliyan uku, da dubu dari uku, da arba’in da bakwai, da dari biyar ( 3,347,500). Don ta siya masa Shinkafa da Waken Suya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matafiya sunyi cirko cirko a Kan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja
A cewar ta, a mai makon wacce ake zarkin tayi amfani da kudin wurin siyar hatsin, sai ta bige da kashe Naira milliyan daya, da dubu dari da arba’in da hudu, da dari takwai, domin amfanin kanta.
Mai shigar da karar ta kuma ce, anbi duk kannin hanyoyin dasu ka dace, domin ganin wacce ake zarkin ta dawo da kudaden, amma abun ya tsutura.
Shaagee ta kuma ce, hakan ya sabawa sashin doka na dari uku da sha uku, kundin dokar Penal code na jihar Benue, na shekarar 2004.
Sai dai, daga bisani bayan kammala karanta karar, wacce ake zargi ta musanta laifukan da ake zarginta dasu.
Hakazalika Mai shari’a Ms Rose Iyorshe ta bada belin wacce ake zargin akan kudi, Naira dubu dari daya, tare da kawo wani babban mutun, wanda yafi karfin kudaden da ake zarginta da su.
Iyorshe ta kuma ce, Mutumin dole ya kasance ma’aikacin gwamnatin jihar Benue, dake mataki na 7 ko sama da haka, kuma mazaunin kusa da garin Makurdi.
A karshe a cewar jaridar Sun, Mai shari’ar kotun, ta dage sauraran karar har izuwa ranar talatin gawatan Yunin da muke ciki.
Comments 1