Daga: Abbas Yakubu Yaura
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Benue (SEMA), Dr. Emmanuel Shior ya bayyana cewa ba’a samu haihuwa jarirai kasa da saba’in a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar ba.
Ya kuma bayyana cewa harin da makiyayan suka kai a jihar kwanan nan ya raba wasu mutane 200 da muhallansu a karamar hukumar Okpokwu ta jihar.
Shugaban SEMA ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a bikin rabon kayan abinci da wanda bana abinci ba duk wata ga ‘yan gudun hijira a fadin jihar, a Makurdi ranar Juma’a.
Da yake magana kan kokarin da ake na dakile yawan haihuwa a sansanonin, ya bayyana cewa “ kalubalen shi ne wanda ke da wuyar shawo kan matsalar domin ko da mutane ba su ci abinci ba, suna da sha’awar yin jima’i; wata bukata ce ta dan Adam da ba za a iya kwacewa daga hannun ‘yan gudun hijirar ba kuma galibinsu suna da matansu tare da su.
“Duk da haka, al’amarin da muke kyama da kokarin shawo kan lamarin shi ne na matasan da ke cikin sansanonin, kwanciya da juna da sauran nau’o’in jima’i da suka haramta a sansanonin.
“Amma tsakanin watan Janairu zuwa yanzu, muna da kusan haihuwa tsakanin 70 zuwa 80 da aka samu,” inji SEMA.
Tun da farko, ya bayyana cewa sansanonin ‘yan gudun hijira da ake sa ran za su ci gajiyar wannan atisayen sun hada da na Makurdi, Guma, Gwer-West, Kwande, Logo da kuma kananan hukumomin Okpokwu na jihar.
Daga cikin kayayyakin da aka raba wa ‘yan gudun hijiran sun hada da buhunan shinkafa 3000; buhunan masarar 1000, buhunhunan Dawa 1000, da kwalayen taliya da buhunan garri da wake guda 1000.
Shior ya ce, “Abin da muke da shi shi ne mu fadada rabon wannan watan zuwa Okpokwu, mu tuna cewa an kai hare-hare kwanan nan a karamar hukumar Okpokwu, don haka mu ma mun kori ‘yan gudun hijira a can. Za mu halarci fiye da mutane 200 da suka yi gudun hijira a wannan al’umma.
“Musamman ina jan hankalin al’ummar duniya da gwamnatin tarayya kan bukatar tallafa wa gwamnatin jihar Binuwai wajen kula da ‘yan gudun hijira.
“Yan gudun hijirar na nan a sansanoni yayin da maharan suka mamaye kauyukansu. Akwai bukatar wadannan ‘yan gudun hijira su koma gidajen kakanninsu amma hakan yana da wahala a yanzu,” in ji shugaban SEMA.
Shior ya tunatar da irin namijin kokarin da gwamnatin jihar ta yi wajen samar da abinci, matsuguni, magunguna da sauran tallafi ga ‘yan gudun hijirar, ba tare da taimakon gwamnatin tarayya ba.