- An haifi wani jariri da yatsu kusan guda takwas a hannunsa
- Iyayen Yaran na ƙoƙarin ganin an yiwa jaririnsu aiki domin dawo masa da yatsunsa kamar na kowa
- Lokitoci sun ce akan samu irin haka a duk 1 cikin 1,000 na haihuwa.
Baby Honghong, mai shekaru 3 wanda a halin yanzu yake zaune a lardin Hubei, an haife shi da yatsu sama da goma sha biyar 15.
A kowannen hannu yana da tafin hannunwa, amma babu babban ɗan yatsa.
Bayan da likitocin asibitocin yankin suka sanar da iyayen Honghong cewa yin tiyatar da za a yi wa wannan jaririn na su, yanayin zai yi matuƙar wahala.
Sun shaidawa iyayen jaririn cewa tiyatar da za a iya yiwa yaran nasu zai ci kuɗi masu dimbin yawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na Manta Na Gaya Wa Mijina Ina Da Naira Miliyan 35 A Asusun Banki Na – Amarya
Hakan yasa a yanzu haka iyayen jaririn ke neman hanyoyin da za su bi domin ganin an yiwa ɗansu tiyatar da zata bashi damar samun hannuwa da ƙafafu kamar kowanne mutum.
A cewar jaridar People’s Daily, Honghong na fama da matsalar polydactyly, yanayin da ake haihuwar yaro da yatsu sama da guda biyar kamar yadda suke bisa ga al’ada.
Likitocin sun shaidawa majiyarmu cewa irin haka na faruwa a kusan 1 cikin 1,000 na haihuwa.
Amma duk da haka, yana da matuƙar wuya sosai kafin a samu wani jariri da irin wannan halittar ta samun yatsu na kafa da hannu da suka haura guda biyar.
An Haifi Jaririn Da Bashi Da Ƙafafu
A WANI LABARIN KUMA: Wani fefen bidiyo mai ban mamaki ya nuna wata jaririyar da aka haifa ba tare da ƙafafu ba sakamakon wata cuta da ba a saba gani ba.
An ɗauki hoton ne a ranar 26 ga watan Yuni a kauyen Sakla, Sironj Tehsil, gundumar Vidisha.
An haifi jaririn da wata cuta mai sa saurin haihuwa da aka fi sani da Tetra-melia, wanda ba a saba gani ba, in da hakan yake haifar da canji na kwayar halittar WNT3 sannan kuma ya haifar da rashin dukkan sassa huɗu na gangar jiki.