Mukaddashin Sifritandan ‘yan sanda na Najeriya wato DPO mai suna Kazeem S Abonde ya bakunci lahira a yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da ‘yan Okada a yankin Ajao da ke jihar Legas.
Rahoanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a yayin da ya jagoranci wata tawagar jami’ansa domin tarwatsa masu tukin babura masu kafa biyun da aka fi sa da ‘yan Okada.
Jaridar Daily Post Nigeria ta ce yayin hargitsin ne jami’ansa suka watse domin buya, lamarin da ya sa abokan fadan na su suka cim ma sa.
Bayanai sun nuna cewa an kone motocin ‘yan sanda biyu a yayin rikicin.
Kafin rasuwarsa shine DPO din Ajangbadi.