An Hallaka Kwastam ɗaya tare da Jikkata 3 bayan masu Ƙwauri sunyi arangama da Jami’ai a Kwara
Wani jami’i mai suna Saheed Aweda ya rasa ransa sannan wasu uku suka samu raunuka yayin da wasu da ake zargin ‘yan fasa kwauri ne suka bude wuta kan jami’an hukumar hadin gwiwa ta (JBPT) na hukumar kwastam ta Najeriya.
An yi zargin cewa maharan sun yi wa jami’an kwanton bauna ne da ke sintiri a karamar hukumar Baruten ta jihar Kwara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dakarun Soji Sun Kama Kwamandojin Boko Haram A Abuja, Kano
Jami’an da suka tsira sun samu munanan raunuka a halin yanzu suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Kakakin hukumar JBPT, reshen jihar Kwara, Chado Zakari, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana lamarin a matsayin ‘musayar wuta’ tsakanin ‘yan fasa kwauri da jami’ansu.
Ya ce, “’Yan ta’addan sun yi kwanton bauna ne kuma suka yi ta harbe-harbe. A musayen wuta da ya barke, daya daga cikin jami’an mu ya mutu, wasu uku kuma suka samu munanan raunuka, amma yanzu haka suna asibiti.”
Da yake ba da labarin abin da ya faru, Chado ya ce JBPT yayin da suke sintiri sun kama buhunan shinkafa 40 na buhunan shinkafa 50kg na kasar waje da kuma jarkokin lita 30 na ruhin mota (PMS) da aka yi watsi da su a hanyar daji kan hanyar Sinau-Kenu, Baruten.
Ya kara da cewa, a lokacin da suke kan hanyar wucewa ne bayan an kwashe kayayyakin da aka kama a cikin “motocin da muka kama domin isar da su dakin ajiyar kaya, wasu gungun ‘yan bindiga sun yi kwanton bauna.
“Sun harbe jami’an mu kai-tsaye, suka caccaki wasu tare da jifan jami’an mu da duwatsu, kwalabe, sanduna da suka hada da laya da sauran muggan makamai.”
Ya ce kodinetan JBPT, Compt. Olugboyega Peters ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cewar sa, “bangaren ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da karfin da ya dace daidai da ka’idojin aiki, sannan kuma za ta bar jami’an ba su da wani abin da ya wuce kare kansu domin amfanin al’umma”.
A wani labarin kuma: Zamfara Ta ɗage Haramci Tarukan Siyasa, ta buɗe Kasuwanni da Makarantu
Gwamnatin Zamfara ta dage takunkumin da ta kaƙaba wa harkokin siyasa a jihar biyo bayan sake bullar barayi da masu garkuwa da mutane.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar ranar Litinin a Gusau.