An Hallaka Sojoji Biyu Da Yan Bokoharam Sha biyu
A kalla Sojoji biyu da Yan Bokoharam Sha biyu suka rasa rayukansu in da suka gwabza yaki a Bula Yobe dake Borno.
A lokacin da ake gwabzawa an sami nasarar kwato manyan makamai gami da harsashi da dama.
KARANTA:-Kotu Ta Yankewa Wani Mai Shekaru 65 Hukuncin Gidan Kaso
Janar Onyema Nwachukwu mai magana da yawun sojojin yace, kamar yadda bayyana ” Rundunar sojojin ta 152 tare da hadin guiwar sojojin sama na HADIN KAI sun fatattaki Yan Kungiyar Bokoharam da ISWAP a lokacin da suke yunkurin Kai hari a Bula Yola dake Borno.
Yan ta’adda sun fito ta inda ba’a tsammani a mashina da Motoci dauke da makamai amma sai dai jajirtattun sojoji sun tunkare su inda suka sasu dole suka koma baya.
Sojojin sunyi nasarar hallaka Yan Bokoharam Sha biyu sun raunata wasu da dama.
Sojojin sun sami nasarar kwato mota mai dauke da bindiga da bindiga self propelled 9 da bindigar Dushika daya da QJC Machine Gun guda daya. Da saura irin su Karamar bindiga da harsashi na bindigar AK47.
Sai dai a lamarin sojoji biyu sun rasu sannan biyar sun samu raunika inda yanzu haka suna asibitin ana kukawa dasu.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban Sojojin Najeriya Faruk Yahaya yace an karo jami’an tsaro tare da makamai don kawo dauki a yankin.
Yace da sojojin dasu kasan ce sun maida hankali tare da hana Yan ta’addan sakewa, tare da dakile duk wani yunkuri na ta’addanci da zasuyi.