An hallaka wasu Yan bindaga tare da kwace muggan makamai a hannun su
Wasu mutane da ake kyautata zaton’yan bindiga ne an hallaka su a garin Kaduna
Shugaban Yan sanda ya bayyana hakane inda sukai sun kurin yin garkuwa da wani Dan Indiya dake garin
KARANTA:- Aisha Bello Matawalle ta tallafawa Mata marasa karfi guda 500
Muhammad Jalinge Mai magana da yawun Yan sanda yace hakan ya auku ne inda sukai ma Dan Indiya kwantan bauna lokacin da zai je Igabi wata Karamar Hukuma dake jahar.
Ya Kara da cewa Yan bindigan sunyi niyyar sai sun tafi dashi sai suka kama harbi kota ko’ina amma hakan bai basu nasara ba saboda Yan sanda sun mayar musu da martani
Ya Kara da cewa dayawa daga cin Yan bindigan sun koma daji da raunuka.