Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta dakile wani hari da aka kai kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar inda suka samun nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai da safiyar yau Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Za Mu Janye Yajin Aiki Ba,Sai An Biya Mu Hakkokin Mu — ASUU
A cewar sanarwar, ‘yan bindigar, wadanda ba su wuce 24 ba, dauke da bindigu kirar AK-47 sun far wa al’ummar garin, inda suka rika harbe-harbe kai-tsaye da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Juma’a tare da yin awon gaba da mutane biyu.
Gambo ya bayyana sunayen mutanen biyu da aka yi garkuwa da su, Alhaji Aminu Wapa da Wada Sale, dukkansu mazauna kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar.
Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Katsina ya bayyana cewa, sakamakon gaggawar amsa kiran gaggawa da rundunar ‘yan sandan ta yi, ta samu nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, inda ya bayyana cewa ana fargabar kashe ‘yan ta’adda da dama a harin da aka dakile.
A cikin sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Idrisu Dabban Dauda, ya yaba da kokarin da jami’an suka yi wajen dakile ‘yan ta’addan, ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a jihar.